Sojojin MDD hudu sun mutu a hannun Anti-Balaka
May 10, 2017Talla
Antonio Guterres a wata sanawar da ya fitar, yace harin an kai shi ne a kan kwambar dakarun kiyayen zaman lafiya inda nan take soja hudu suka mutu wasu kimanin 10 aka kai su babban asibiti a Bangui babban birnin Kasar. Sanarwar ta kara da cewa kawo yanzu akwai soja guda wanda ya bace bayan harin. Ana dai tuhumar 'yan kungiyar anti-Balaka da ke zama mayakan kiristoci da kai farmakin. Lamarin ya farune a kan iyakar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango