1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin kiyaye zaman lafiyar AU sun mutu a Darfur

Amurka tayi Allah wadai da kisan dakarun sojin kungiyyar hadin kann kasashen Africa da akayi a yankin Darfur na kasar Sudan.

Bisa hakan , tuni kasar ta Amurka ta bukaci gwamnatin kasar data bawa tawagar kiyaye zaman lafiyar goyon bayan daya kamata, wajen ci gaba da gudanar da aikin su, a hannu daya kuma da cafke wadanda suka aikata wannan aiki don hukumta su.

Kisan sojojin kiyayen zaman lafiyar biyu da kuma jikkata wasu uku, ya biyo bayan wani mamaye ne da yan tawayen yankin da ba a san kosu wanene ba suka kai musu a yankin na Darfur.

Wannan dai rikici na Darfur daya ki ci yaki cinyewa , ya zuwa yanzu yayi sanadiyyar rayuka a kalla sama da dubu dari 2, wasu kuma miliyan biyu sun yi kaura don tsira da rayukan su.