Sojojin kawance a Afghanistan sun kashe mayakan Taliban akalla 80 | Labarai | DW | 24.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin kawance a Afghanistan sun kashe mayakan Taliban akalla 80

Rahotanni daga Afghanistan sun ce dakarun kawance dake karkashin jagorancin Amirka sun samu nasara a farmakin da suke kaddamar kan ´yan tawayen kungiyar Taliban. Kakakin rundunar Amirka ya ce an kashe ´yan tawaye fiye da 80 musamman a kudancin kasar ta Afghanistan. A batakashin da aka kwashe sa´o´i da dama ana yi a jiya a kusa da garin Mirabad dake lardin Uruzgan an halaka akalla ´yan tawaye 40.