Sojojin Jamus sun kama hanyar zuwa Kongo | Siyasa | DW | 10.07.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sojojin Jamus sun kama hanyar zuwa Kongo

A yau ne tawagar farko ta dakarun kasar Jamus ta bar Jamus zuwa jamhuriyar demokradiyar kongo,a matsayin wani bangare na sojojin kungiyar taraiyar turai da zasu sanya ido a zaben kasar

default

Sojoji 60 ne dai suka bar birnin Cologne zuwa birnin Libraville na kasar gabon makwabciyar Kongo,ya zuwa ranar 18 ga watan na yuli sauran sojin na jamus zasu isa zuwa Kongo da Gabon,inda zasu hade da dakarun majalisar dinkin duniya su 17,000 da tuni suke kasar.

Sojojin na Jamus,suna bangare ne sojin kungiyar taraiyar turai 2000 da zasu kasance masu sanya ido a zabe karo na farko bisa turbar demokradiya a Kongo a ranar 30 ga watan yulin nan da muke ciki.

A yau din ne sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan,ya kai ziyara a hedkwatar dakarun kungiyar taraiyar turai a garin Potsdam kusa da birnin Berlin,yayinda dakarun Faransa wadda suka fi yawa cikin sojin kungiyar,su zasu kula da sansanin sojojin dake birnin Kinshasa.

Kimanin sojojin jamus 100 sun kafa sansaninsu a Kinshasa cikin wata daya gabata domin shirya karbar dakarun na kungiyar taraiyar turai.

Lokacin ziyarasa zuwa Kinshasa a makon daya gabata,ministan tsaro na jamus Franz Josef Jung,yace dalilin aikewa da wadannan sojoji shine tabbatar da an gudanar da zabe ba tare da wata matsala ba.

Wannan shine karo na farko da Jamus zata taba aikewa da dakarunta gudanar da wasu aiyukan zaman lafiya a nahiyar Afrika tun bayan aiyukan jin kai na majalisar dinkin duniya a kasar Somalia a 1993.

A halin da ake ciki kuma,wata kungiyar kare hakkin bil adama tayi kira da a tsare wani janar na soji da yayi bore a kasar,tana mai baiyana tsaron kada ya kawo cikas ga zaben da zaa gudanar.

Kungiyar wadda ake kira VSV tace janar din yana da muggan makamai,da naurorin sadarwa irin na zamani wanda akayi sumogarsu daga kasar Rwanda.

Rahotanni sunce janar Nkunda dan kabilar tutsi,ya hada kai da kasar Rwanda a lokacin bore da akayiwa gwamnatin Laurent kabila,yanzu kuma ana nemansa a kotun kasa da kasa da aikata laifukan yaki,wanda dakarunsa suka aikata a lokacinda suka mamaye Bukavu a 2004.

Wani jamiin majalisar dinkin duniya ya kiyasta cewa janar Nkunda yana da dakaru kusan 2000,hakazalika kuma yana karbar makamai daga kasar Uganda.

Kungiyar kare hakkin bil adaman tace,ya kamata a karawa sojojin kasar karfi da makami,domin kare duk wani hari da dakarun Nkunda zasu iya kaiwa a lokacin wannan zaben.

 • Kwanan wata 10.07.2006
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtzI
 • Kwanan wata 10.07.2006
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtzI