Sojojin Jamus sun hallaka wasu dakarun Afghanistan shidda | Labarai | DW | 03.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Jamus sun hallaka wasu dakarun Afghanistan shidda

Sojojin Jamus sun hallaka wasu dakarun Afghanistan shidda a Arewacin ƙasar bayan da taliban ta kashe wasu sojojin Jamus Uku

default

Wani Sojin jamus yana bada umarni a Afghanistan

Sojojin Jamus sun hallaka wasu dakarun Afghanistan shidda. Sojojin na Jamus dai sunce sunyi zaton Sojojin Taliban ne ke ƙoƙarin kai masu hari, bayan da suka umarce su dasu tsaya amma kuma sukaci gaba da tunkaro su, abinda yasasuka buɗe masu wuta.

Koda yake Hukumomin Sojin Afganista dana NATO sun tabbatar da mutuwar Sojojin Afghanistan shidda, amma na Jamus sunce Sojoji biyar ne suka rasu.

A waje ɗaya kuma Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana damuwar ta da kisan wasu Sojojin Jamus uku a ƙasar Afganistan.

Kafofin ma'aikatan tsaron Jamus na cewar kimanin Sojojin Jamus uku ne aka kashe kana wasu 8 suka samu raunuka bayan da dakarun Taliban kimanin 100 sukayi masu kwantar ɓauna a kusa da garin Kunduz dake Arewacin ƙasar.

Wannan harin dai shine mafi girma da aka kaiwa Sojojin na Jamus tun lokacin da Sojojin ƙawancen suka isa Afganistan a shekara ta 2001. A wata sanarwa da ƙungiyar ta Taliban ta fitar tasha alwashin cigaba da kai farmaki akan Sojojin na Jamus muddin dai basu fice daga ƙasar ba.

Mawallafi : Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadisou Madobi