Sojojin Jamus A Kasar Jibuti | Siyasa | DW | 11.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sojojin Jamus A Kasar Jibuti

Kimanin sojojin ruwa 200 Jamus ta tsugunar a kasar Jibuti a karkashin matakin yaki da ta'addanci na hadin guiwa da aka gabatar sakamakon hare-haren nan na 11 ga watan satumban shekara ta 2001

Sojojin Jamus akan hanyarsu ta zuwa Jibuti

Sojojin Jamus akan hanyarsu ta zuwa Jibuti

Kowane daga cikin mayakan ruwa na Jamus su kimanin 200 da aka tsugunar a kasar Jibuti, ya kan yi aiki ne na tsawon watanni shida kafin a maido da shi gida. Jirgin ruwan yakin dake dauke da su mai tsawon mita 130 yana kuma dauke da jiragen sama masu saukar ungulu guda biyu, wadanda kan yi shawagi a samaniyar yankin domin bin diddigin jiragen ruwan dake zirga-zirga a mashigin tekun bahar maliya. A lokacin da take bayani daya daga cikin sojojin tayi nuni ne da cewar babban abin dake ci mata tuwo a kwarya shi ne kasancewar mutum ba ya samun sararawa ko da ta minti daya. Sai kuma matsalar zafin yanayi mai radadin gaske. Kasar Jibuti na daya daga cikin kasashen da suka fi zafin yanayi a duniya kuma sojojin na Jamus na fama da wannan radadi, inda wani sojan ya ce ya kan aiwatar da lita bakwai na ruwa a rana. Amma duk da haka akwai wasu daga cikin sojojin dake bayyana gamsuwa da aikinsu a mashigin tekun bahar-maliya. Masu fama da matsala sun hada da ma’aurata, wadanda suka baro matansu kuma ba su da wata kafa ta kai ziyara har sai bayan sun kammala aikinsu na tsawon watanni shida. Wannan mawuyacin hali ya haddasa mutuwar aure da dama. Domin tinkarar wannan matsala mahukunta na sojan Jamus kan ba da wata dama ga matan aure domin ganawa da mazajensu har tsawon mako daya a tsuburin Seychells. Amma fa ba zamantakewar iyali ce kadai ke addabar sojojin ba, su kan sha fama da kewar abubuwa da dama na rayuwa da suka saba yau da kullum. Wani abin lura kuma shi ne sojojin ba sa manna alamar suna a jikin rugunansu saboda dalilai na tsaro. Domin kuwa nauyin da aka dora musu shi ne yaki da ta’addanci kuma a saboda haka ya zama wajibi su kauce daga duk wani abin da ka iya zama barazana ga makomar rayuwarsu. Sojojin kan sa ido akan jiragen dake kai da komo a mashigin tekun bahar maliya su kan kuma tsayar da wasu daga cikin jiragen da ake munana zato a game da su domin bincike. To sai dai kuma binciken na gudana ne tare da amincewar kaftin din jirgin da lamarin ya shafa. Idan kaftin din bai ba da izini ba, sai sojojin su janye sannan a yi rajistar jirgin a tsakanin jiragen ruwan da ake tababa game da al’amuransu. Bayan wannan rajista jirgin zai iya fuskantar kalubala daga jiragen ruwan yakin kasashen taron dangi domin yaki da ta’addanci, wadanda suka hada da Amurka da Birtaniya da kuma Faransa. Ko da yake sojojin na Jamus su kan binciki dukkan jiragen ruwan safara dake ratsa mashigin na bahar-maliya, amma kawo yanzu babu wani jirgin da aka same shi yana dakon makamai. Matsalar dake akwai shi ne na kasancewar ba wanda zai iya tantance dan ta’adda, musamman ma idan aka ba da la’akari da masu safarar miyagun kwayoyi da ‚yan fashin jiragen ruwa, wadanda galibi sune sojojin kan cafke su. Akalla dai an samu tsaro iya gwargwado a mashigin tekun tsakanin Jibuti, Somaliya, Yemen da Oman. Kuma ta la’akari da haka ana iya cewa kwalliya ta mayar da kudin sabulu akan manufa.