1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sojojin Jamus A Afghanistan

Jamus zata ci gaba da tsugunar da sojojinta dake aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Afghanistan duk da harin baya-bayan nan da aka kai musu

Ministan tsaron Jamus a ziyarar da ya kai wa sojojin kasar a Kunduz

Ministan tsaron Jamus a ziyarar da ya kai wa sojojin kasar a Kunduz

Duk da harin da aka kai kan wata mota ta sojan kiyaye zaman lafiya na Jamus, amma gwamnati ta ce sojojin zasu ci gaba da gudanar da ayyukansu a Kunduz ta kasar Afghanistan. A jiya laraba da sanyin safiya wata nakiya tayi bindiga a garin na arewacin kasar Afghanistan a daidai lokacin da wata motar sojan Jamus ke wucewa kuma matukin motar da wasu farar fula ‚yan kasar Afghanistan su uku da motar ke dauke da su duk sun mutu nan take. Babu dai wani soja ko da guda daya a cikin motar. To sai dai kuma duk da wannan barazana an saurara daga bakin Hannes Wendroth dake magana da yawun ma’aikatar tsaron Jamus yana mai fadi cewar kasar ba zata janye sojojin nata daga Kunduz ba, zasu ci gaba da gudanar da ayyukansu na tsaron lafiya da sake gina kasar ta Afghanistan, wacce yaki yayi kaca-kaca da ita. Tun da farkon fari sojojin na Jamus suka hakikance cewar garin na Kunduz ba ya da kwanciyar hankali kuma wajibi ne su rika taka tsantsan kuma harin na jiya laraba ba shi ne na farko da aka fuskanta ba. A makon da ya gabata an kai farmaki tare da kisan wasu ma’aikata ‚yan kasar China su 11 a daidai lokacin da suke barci. To amma bisa ga ra’ayin ma’aikatar tsaron Jamus, wannan mawuyacin hali na zaman dardar da ake ciki, wanda kuma ga alamu yake da nasaba da karatowar wa’adin zaben kasar ta Afghanistan ya sanya ci gaba da aikin sojojin kiyaye zaman lafiyar yake da muhimmanci matuka ainun. A halin yanzu haka ana shirye-shiryen bude karin sansanin sojan kiyaye zaman lafiyar na Jamus a yankin arewa-maso-gabacin Afghanistan. Ana shawarar kafa sansanin a wani gari wai shi Faizabad, wanda shi ne ya fi daukar hankalin sojan kiyaye zaman lafiyar na Jamus a baya ga garin Kunduz. To sai dai kuma ganin nisan wannan yanki da wuya sojojin, wadanda yawansu bai wuce 250 ba su samu wata kafa ta kiyaye zaman lafiyarsa. Mai yiwuwa a tura wasu karin sojojin zuwa yankin nan ba da dadewa ba. A lokacin da yake bayani game da haka kakakin ma’aikatar tsaron Jamus Wendroth cewa yayi:

A halin yanzu muna shawartawa tare da sauran kasashen dake da hannu a matakan sake gina kasar Afghanistan a game da tura wata sabuwar tawaga zuwa Kunduz. To sai dai kuma babu wani karin bayanin da zan iya yi game da haka. Ala-ayyi-halin muna nazari game da Faizabad kuma mai yiwuwa a samu wanzuwar sojojin a can nan ba da dadewa ba.

A yanzun dai babu wani haske da aka samu a game da ko shin tawagar zata zama ta hadin guiwa ce ko kuwa ta sojan Jamus su ya su. An sha yin batu a game da kasar Netherlands, amma ga alamu ita kanta kasar zata tura tata tawagar zuwa Afghanistan. Tuni dai ‚yan hamayya a nan kasar suka fara sukan lamirin wannan shiri na tura karin sojojin Jamus zuwa Afghanistan saboda matsalar tsaro. A ganinsu wajibi ne a yi bitar lamarin domin a tantance amfani da kuma rashin amfaninsa.