Sojojin Jamus 3 sun rasa rayuka a Afghanistan | Labarai | DW | 19.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Jamus 3 sun rasa rayuka a Afghanistan

A ƙalla mutane 9, da su ka haɗa da sojoji 3, na ƙasar Jamus, su ka rayuka a cikin wani harin da ya wakana a tsakiyar kasuwar Kunduz, dake yankin arewancin Afghanistan.

Hatsarin ya rutsa da wannan sojoji, a yayin da su ke saye-saye cikin wannan kasuwa.

Mayaƙan Taliban sun bada sanarwar ɗaukar alhakin kai wannan hari.

Daga Berlin, babban birnin tarayar Jamus, ministan tsaro Franz Josef Yung, ya bayana matuƙar damuwa a game da wannan kissa:

„Wannan al´ammari ne, na matuƙar ɓacin rai, wanda kuma zai sa mu ƙara tunani a game da makomar sojojin mu, a wannan yankin na ƙasar Afghanistan, mai ƙunshe da babban hatsari ga rundunbar mu.

Mu na issar da ta´aziya zuwa ga iyalan sojojin da su ka rasa rayuka“.

Wannan saban hari ya biwo bayan sanarwar da komandan rundunar sojojin NATOn ya bayar mai nuni da cewa, a ƙalla yan taliban 70 su ka rasa rayuka, wasu da dama su ka ji raunuka, a sakamakon arangamar da a ka gwabza a daren jiya juma´a.

A cewar wannan sanarwa, ɓangarorin 2 sun yi fito na fito, a yanki Samkanai da ke kussa da iyaka da ƙasar Pakistan.