SOJOJIN IVORY COAST DA NA FARANSA......... | Siyasa | DW | 01.12.2003
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SOJOJIN IVORY COAST DA NA FARANSA.........

Dakarun kasar Ivory Coast sun bukaci sojojin faransa dake tabbatar da darajawa yarjejeniyar tsagaita wuta dasu gaggauta tattara yansu yanasu domin barin yankunan da suke domi basu daman yakan yan tawayen da har yanzu ke rike da arewacin kasar.Sojojin sunyi wannan kiran ne kai tsaye ta gidan talabijin din wannan kasa. Kiran nasu yazo yini guda bayan dakarun Faransan sun cimma watsar da wasu yan tawaye dake machi da sojojin Ivory coast din,weadanda kuma suka doshi garin Bouake dake tsakiyar wannan kasa dake yammacin Afrika.kafofin yada labaru sun yayata cewa akalla mutane shida suka samu rauni kana an lalata wata motar sojin guda a wannan yamutsi.A nasu bangare sojojin faransan sun tabbatar da budewa masu zanga zangan wuta,a matsayin barazanar watsar dasu..

Sanarwar dakarun kasar na nuni dacewa basa bukatar sojojin na faransa domin su kadai zasu iya maganta yan tawayen cikin yini biyu. Wannan sabon rikici dai ya dada kawo fargaba tsakanin jamaar wannan kasa dake da arzikin coco ,kasar da har yanzu ke rabe sakamakon rikicin yunkurin juyin mulki daya fara tun a shekaran daya gabata. Bayan an cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Ivory coast,a halin da ake ciki yanzu akwai kimanin dakarun Faransa dubu 4 tare dana wasu kasashe a yammacin Afrika kimani 1,300,domin tabbatar dacewa baa samu akasin wannan yarjejeniya ba.

Tun a watan Yuli aka kawo karshen fadan,amma akwai rashin yarda da juna a tsakanin gwamnatin kasar da yan tawayen da har yanzu ke rike da yankunan arewacin kasar. A nasu mayar da martani a birnin Paris kakakin sojin Christian Baptiste yace kalaman na sojojin Ivory Coast barazanar bance da bata tushe.Sojojin Kasar da suka kutsa gidan talabijin din Abidjamtare da yin wannan sanarwa,sun tabbatar goyon bayansu wa shugaba Laurent Gbagbo,kana sunyi mkira ga hafsan sojin kasar General Mathias Doue da sauran manyan hafsoshin dasu gaggauta yin murabus daga mukamansu. Su kuwa dakarun faransa dake Ivory Coast cewa sukayi sun dakatar da wannan yamutsi na ranar asabar ne bisa ga umurnin hukumomin kasar,ayayinda kafofin yada labaru sukace General Doue na bada umurnin dakatar da wannan zanga zanga. Rahotanni na nuni dacewa shugaba Laurent Gbagbo ya gana da masu bashi shawarwari kann harkokin tsaro a Abidjam.Jite jite daga wannan kasa dai na nuni dacewa jamaa na cigaba da zama cikin fargabar sake barkewan fada,bayan yan tawayen sunki mika makaman nasu,ayayindfa magoya bayan Gbagbo ke ganin kamata yayi a kore su daga wannan kasa.

 • Kwanan wata 01.12.2003
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvnK
 • Kwanan wata 01.12.2003
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvnK