Sojojin Isra´ila sun kame Falasdinawa 18 a samame da suka kai a Ramallah | Labarai | DW | 07.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Isra´ila sun kame Falasdinawa 18 a samame da suka kai a Ramallah

A wani samame da suka kai a hedkwatar hukumar leken asiri ta rundunar sojin Falasdinawa dake birnin Ramallah, sojojin Isra´ila sun kame Falasdinawa 18. Wani kakakin rundunar sojin Isra´ila ya ce ana zargin mutanen da hannu wajen yin garkuwa da sojoji da kuma farar hular Isra´ila tare da shirya kai hare hare akan Isra´ila. Bugu da kari sojojin Isra´ila sun kwace makamai masu tarin yawa. Da sanyin safiyar yau wasu motocin sojin Isra´ila suka yiwa ginin hedkwatar ta sojin Falasdinawa kawanya. Rahotanni sun yi nuna da cewa mutanen da aka kaman ´ya´yan kungiyar Baradan al-Aqsa ne.