Sojojin Isra´ila sun kai wani gagarumin samame a birnin Nablus | Labarai | DW | 25.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Isra´ila sun kai wani gagarumin samame a birnin Nablus

A wani samame mafi girma cikin shekaru biyu tankokin yakin Isra´ila da dama sun kutsa cikin birnin Nablus na Gabar Yamma da Kogin Jordan. Dakarun tsaron Isra´ila sun kame akalla mutane 30 sannan suka hana dubun dubatan Falasdinawa fita daga gidajen su. An kashe sojojin Isra´ila biyu a fashewar wani bam a lokacin wannan samame, wanda aka kai a matsayin martani da gano wani dakin harhada bama-bamai a birnin a jiwa asabar. A kuma can Zirin Gaza an kashe akalla Falasdinawa 4 tare da jiya 20 rauni sakamakon barkewar sabon fada tsakanin magoya bayan kungiyoyin Hamas da Fatah wadanda ba sa ga maciji da juna. Fadan dai shi ne irinsa mafi muni tsakanin kungiyoyin tun bayan da sassan biyu suka amince da kafa gwamnatin hadin kan kasa kusan makonni 3 da suka wuce.