1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Iraki sun shiga birnin Ramadi

Salissou BoukariDecember 22, 2015

A wannan Talata ce dai a wani mataki na nuna samun nasara a yakin da suke da 'yan kungiyar IS, dakarun sojan Iraki suka kutsa kai birnin Ramadi.

https://p.dw.com/p/1HRwU
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Mai magana da yawun ofishin kula da yaki da ta'addanci na kasar ta Iraki Sabah Al-Nomane, ya ce a halin yanzu sun shiga birnin na Ramadi kuma sannu a hankali za su bi unguwa-unguwa domin tsabtace birnin daga duk wasu 'yan ta'addan da suka rage. Birnin na Ramadi da ke a nisan km a kalla 100 a Yammacin birnin Bagadaza, ya fada a hannun mayakan na kungiyar IS ne tun a watan Mayu da ya gabata. A makon da ya gabata dai shugaban sojojin kasar ya ce abun da ya rage na mayakan na IS a birnin bai fuce mutun 250 zuwa 300 ba wanda sannu a hankali za su kakkabe su daga wannan birni.

Daga na shi bangare mai magana da yawun sojojin kawancen da ke kasar ta Iraki Kanal Steve Warren, ya ce jiragensu sun yi ruwan bama-bamai har sau shidda a yau din nan kan mayakan na IS a yankin na Ramadi.