Sojojin gwamnatin Sri Lanka na yiwa yankunan ´yan tawaye ruwan bamabamai | Labarai | DW | 16.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin gwamnatin Sri Lanka na yiwa yankunan ´yan tawaye ruwan bamabamai

Sojojin Sri Lanka sun sake kai farmaki akan garin Kilinochi wanda ya kasance sansanin ´yan tawayen Tamil Tigers dake arewacin kasar. Hakan na matsayin martani ga wani mummunan hari da aka kai kan wata safa a ranar alhamis wanda yayi sanadin mutuwar mutane 64 sannan wasu dama suka jikata. Babban sakataren MDD Kofi Annan yayi kashedi game da rura wutar wani yakin basasa a kasar, sannan a lokaci daya yayi kira ga sassan biyu da su koma ga girmama yarjejeniyar tsagaita bude wuta. To amma a nasa bangaren ministan harkokin wajen Sri Lanka Mangala Samaraweera cewa yayi yanzu hakurinsu ya kai makura, a saboda haka ya zama wajibi gwamnati ta dauki takaitattun matakai na tsoratarwa.