Sojojin gwamnatin Chadi sun kutsa cikin garin Abeche | Labarai | DW | 26.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin gwamnatin Chadi sun kutsa cikin garin Abeche

Rundunar sojin Chadi ta yi ikirarin sake kwace birni mafi girma dake gabashin kasar, inda ake fama da rikici, kwana daya bayan da ´yan tawaye da ke son kifar da gwamnati suka ce sun kwace garin. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce dakarun gwamnati sun kutsa cikin garin na Abeche mai nisan kilomita 885 gabas da Njamena babban birnin Chadin. Sannan ´yan tawaye sun ranta daga cikin na kare, sa´o´i kalilan gabanin shigar dakarun gwamnati. Garin na Abeche daiy a kasance cibiyar kungiyoyin ba da agaji da dama wadanda ke kula da ´yan gudun hijira kimanin dubu 200 daga lardin Darfur na Sudan da kuma wasu ´yan Chadi kimanin dubu 50 da suka rasa muhallinsu.