Sojojin gwamnati sun kai farmaki akan ´yan tawaye a lardin Ituri | Labarai | DW | 25.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin gwamnati sun kai farmaki akan ´yan tawaye a lardin Ituri

A kasar JDK dakarun MDD da takwarorinsu na Kongo su kimanin dubu 1 da 900 sun sake kwace garin Nioka dake lardin Ituri na gabashin kasar, daga hannun ´yan tawaye. Rahotanni sun ce an halaka sojin sa kai guda 30 yayin farmakin hadin guiwar da sojojin MDD da na gwamnatin Kongo suka kai. To sai dai madugun sojin sa kai Peter Karin wanda ya mayar da garin Nioka sansaninsa, ya tsere. Ana zargi sojin sa kan karkashin jagorancin Karim da aikata ta´asa akan fararen hular wannan yanki. Wannan farmakin ya zo ne a daidai lokacin da sakamakon kuri´ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar ya nuna cewa ilahirin ´yan kasar sun amince da shi.