Sojojin Faransa sun isa a kudancin Lebanon | Labarai | DW | 19.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Faransa sun isa a kudancin Lebanon

A kuma can kudancin Libanon din sojoji Faransa su guda 50 sun isa garin Naqura ta ruwa a matsayin dakarun farko na rundunar da MDD zata girke a yankin kudancin Lebanon. Faransa dai ta yi alkawarin ba da gudunmawar dakaru 200 ga rundunar MDD dubu 15 kamar yadda aka amince a kudurin da ya tanadi tsagaita wutar. Mukaddashin babban sakataren MDD Mark Malloch Brown yayi kira ga kasashen Turai da su matsa kaimi wajen hada kan sojoji dubu 3 da 500 a cikin kwanaki 10.

Ya ce “Muna son wannan ta kunshi dakaru daga kasashe dabam dabam don ta samu amincewa daga sassan biyu. Saboda haka tun da farkon fari muka ce ya kamata wannan runduna ta kasance tana da dakaru na kasashe Turai da na musulmi, domin biyan bukatun dukkan bangarorin biyu.”