1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Burtaniya sun janye daga Basra

Sojojin kasar burtaniya sun kammala janyewa daga birnin Basra dake kudancin kasar Iraqi.Wata majiya daga maaikatar tsaro a birnin London tace kimanin sojoji 500 ne zasu koma wani babban sansani na Burtaniya dake wajen birnin na Basra.Wannan babban jamiin sojin Burtaniyan yace sojojin na Burtaniya sun mika harkokin gudanar da tsaro a fadar da hedkwatar tasu take ga hannun dakarun kasar Iraqi.Sojojin Burtaniya kimanin 5,500 suke Iraqi yawancinsu kuma a Basra.Sai dai kuma wasu mazauna birnin na Basra sun baiyana tsoronsu cewa fada tsakanin kungyiyo hamaiya masu dauke da makamai zai karu bayan janyewar sojin na Burtaniya.