Sojojin Amurka sun kama wakilin gidan talabijin na Al-Jazeera a Afghanistan | Labarai | DW | 01.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Amurka sun kama wakilin gidan talabijin na Al-Jazeera a Afghanistan

Arrest/Aljazeera

A Afghanistan sojojin Amurka sun kama wakilin gidan talabijin na Al -Jazeera tare da mai daukar masa hotuna da kuma direbansa.

Tashar talabijin din da ke da mazauninta a kasar Qatar ta ruwaito sojojijin Amurka suna cewa bayanda suka damke Waliyullah Shaheen da shi da tawagar sa sun mika shi ga yansandan kasar ta Afghanistan.

Sojojin na Amurka sunce sun kama dan jaridar da abokan aikin nasa ne saboda suna daukar hoton wuraren da suka shafi tsaro da ke kusa da hedikwatar dakarun kasashen waje da Amurka ke jagoranta a kasar.

Tashar ta Al-Jazeera tace a yanzu dai tana kan duba bayyanai akan lamarin.