Sojojin Amurka goma sun rasa rayukansu a Falluja | Labarai | DW | 02.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Amurka goma sun rasa rayukansu a Falluja

Wasu sojojin Amurka guda 10 sun rasa rayukansu wasu kuma 11 suka samu rauni a birnin Falluja.

Rundunar sojin Amurkan tace,sojojin suna kan wani sintiri ne a lokacinda wani bam ya fashe a birnin na Falluja.

A halin da ake ciki kuma,kimanin yan sunni da yan shia su 1000 suka yi sallah tare a birnin Bagadaza,domin nuna hadin kansu.

Bayan Sallar jumaar kungiyoyin biyu sun gudanar da zanga zanga suna masu yin Allah wadai da hare haren da ake kaiwa,tare kuma tsare mutane barkatai ana zarginsu da kaiwa wadannan hare hare.