Sojojin Amurika 20 sun mutu a Irak | Labarai | DW | 21.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Amurika 20 sun mutu a Irak

Sojojin Amurika 5 su ka sheƙa lahira, sannan da dama su ka ji mummunan raunuka, da sanhin sahiyar yau lahadi, a ƙasar Iraki.

Idan kuma ba manta ba, a jiya wani jirgin sama mai durra agullu, ɗauke da sojojin Amurika ya yi salla da ka, inda take !!! 13 su ka ce ga garin ku nan.

Wannan itace assara mafi muni, da Amurika ta fuskanta a Irak, tun bayan da shugaba Georges Bush, ya bayyana saban tsarin sa, na ƙara sojoji dubu 20, a ƙasar, tsarin da ya ci karro, da kakkausar adawa, daga jama´iyar Demokrates, mai rinjaye a majalisar wakilan Amurika.

Tashe-tashen hankulla a Irak sun ƙara ƙamari, duk da mattakan tsaron da hukumomin ƙasar su ka ɗauka, albarkacin sallar Ashura, da ke farawa yau ɗin nan , inda a tsawan kwanaki 10, musulmi mabiya ɗarikar Schi´a, za su tunani, tare da nuna alhini ga mutuwar imman Husain, jikan Manzan Allah, tsira da aminci Allah, su ƙara tabbata a gare shi.