Sojojin Ammirka guda 3 sun sheka lahira bayan tashin wani bam kusa da ayarin motocinsu a Iraqi. | Labarai | DW | 20.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Ammirka guda 3 sun sheka lahira bayan tashin wani bam kusa da ayarin motocinsu a Iraqi.

Rahotannin da ke iso mana daga Iraqi na nuna cewa sojojin Amirka guda uku ne suka sheka lahira, sa’annan wani daya kuma ya ji rauni, yayin da wani bam da aka dasa a gefen titi ya tashi kusa da ayarin motocinsu a garin Balad, mai nisan kimanin kilomita 70, a arewacin birnin Bagadaza. Hukamar rundunar sojin Amirka a Iraqin, ta tabbatad da rahotannin, inda ta kara bayyana cewa, a jiya da yamma ne wannan lamarin ya auku, kuma ana yi wa sojan da ya ji raunin jiyya a asibiti.

Kawo yanzu dai, alkaluman da ma’aikatar tsaron Amirkan, wato Pentagon ta bayar, na nuna cewa, yawan sojojin kasar da suka rasa rayukansu a Iraqi, tun da Amirkan ta jagoranci kai wa Iraqin hari a cikin watan Maris na shekara ta 2003, ya tashi zuwa dubu da dari 9 da 79.

Tun ran asabar da ta wuce kuma, wato ranar da aka gudanad da zaben raba gardama a Iraqin, sojojin Amirka guda 12 ne aka kashe, a fafatawar da suke yi da `yan yakin gwagwarmayar kasar.