1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Amirka sun kashe mutane biyar a unguwar Sadr City

Jami´an sojin Amirka sun ce dakarun su sun kashe sojojin sa kai 5 sannan sun kame daya a wani samame da suka kai a unguar Sadr City dake birnin Bagadaza. Wata sanarwa sojin Amirka ta ce ana zargin mutumin da aka kaman da alaka da rundunar juyin juya hali ta kasar Iran. To sai dai wani jami´in ma´aikatar tsaron Iraqi ya ce wani farmaki da aka kai ta sama don ba da kariya da masu kai samamen, ya afkawa wasu motoci da suka yi layin sayen man fetir, kuma wadanda aka kashen fararen hula ne wadanda ba su san hawa ba su san sauka ba.