1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Amirka sun aikata laifin yaki a Afghanistan

Salissou BoukariOctober 6, 2015

Shugabar kungiyar Likitocin duniya ta Medecin sans Frontieres Joane Liu, ta zargi sojojin Amirka da aikata laifin yaki bayan hari da suka kai a ofishinsu na birnin Kunduz..

https://p.dw.com/p/1Gjca
Janar John Campbell
Janar John CampbellHoto: picture-alliance/dpa/S. Thew

Shugabar ta Medecin sans Frontieres ta kara da cewa, labarin da 'yan kasar Afghanistan suka bayar na cewa 'yan Taliban na fake wa da wannan babban asibiti suna kai hare-hare, ya nunar cewa harin da aka kai ba bisa kuskure ne ba. A wannan Talatar ce kuma Janar John Campbell, babban kwamandan sojojin kasar ta Amirka da kuma na kungiyar tsaro ta NATO ya sanar cewa sojojinsu sun kai hari a ranar Asabar da ta gabata, ga wani babban asibiti na Medecin sans Frontieres da ke birnin Kunduz bisa kuskure, harin da ya yi sanadiyar rasuwar mutane 22.

Tuni dai ma'akatar shari'a ta kasar Amirka ta sanar da aniyarta ta gudanar da bincike kan lamarin, yayin daga nashi bangare shugaban kasar Barack Obama ya ce ya kyautu a yi taka tsan-tsan na ganin irin haka bai kara faruwa ba a nan gaba.