Sojojin Amirka goma sun rasu a hadarin alikofta a Afghanistan | Labarai | DW | 06.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Amirka goma sun rasu a hadarin alikofta a Afghanistan

Wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakin sojin Amirka yayi hadari a gabashin Afghanistan, inda ya halaka dukkan mutane 10 dake cikin sa. Jirgin yayi hadarin ne lokacin da yake kai farmaki jiya daddare a kusa da birnin Asadabad, hedkwatar lardin Kunar dake gabashin Afghanistan. Ko da yake rundunar sojin Amirka ta ce ba abokan gaba ne suka harbo alikoftan yakin ba, amma ´yan tawayen Taliban sun ikirarin kakkabo jirgin. Amirka dai ta girke sama da dakaru dubu 19 a Afghanistan a cikin shirinta na yaki da ´yan ta´adda na kasa da kasa.