Sojojin Amirka a Iraki sun tsare mutane 60 a Bagadaza | Labarai | DW | 12.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Amirka a Iraki sun tsare mutane 60 a Bagadaza

Dakarun Amirka a birnin Bagadaza sun kai wani samame a wani wurin zaman makoki inda suka kama mutane 60 da ake zargi da alaka da bangaren kungiyar al-Qaida da ke da hannu a jerin hare haren bama bamai da ake kaiwa da mota. Wannan dai shi ne samame mafi girma tun lokacin Amirka ta tsananta matakan tsaro a Bagadaza a wani mataki na murkushe masu ta da zaune a babban birnin na Iraqi. Wata sanarwa da rundunar sojin Amirka ta bayar ta ce an yi kamen ne a unguwar Arab Jabour dake kudancin Bagadaza wanda kuma ya kasance sansanin sojojin sa kai na ´yan Sunni. Sanarwar ta ci-gaba da cewa an yi amana mutanen su 60 na da alaka da wani shugaban kungiyar al-Qaida a Iraqi wanda ya kware wajen harhada bama-bamai.