1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Amirka a Iraƙi sun kai samame kan ofishin wakilan Iran

Dakarun Amirka sun kai samame a ofishin karamin jakadancin Iran dake birnin Arbil na ´yan Kurdawa dake arewacin Iraqi inda suka kame mutane 5. Baya ga haka dakarun na Amirka sun kama kwace wasu takardu da na´u´rori masu kwakwalwa a yayin da hukumomin tsaro na Kurdawa suka toshe dukkan hanyoyin dake zuwa wurin da ginin yake. A martanin da ta mayar gwamnati a birnin Teheran ta kira ´yan diplomasiya dake wakiltar wasu cibiyoyin Amirka da su yi mata bayani. An kai samamen ne a daidai lokacin da Amirka ke zargin hukumomin Iran da rura wutar rikicin Iraqi tare da ba da umarnin kai hare hare akan dakarun Amirka.