Sojojin Afghanistan 40 sun ji rauni sakamakon tashin wani bam kusa da motarsu. | Labarai | DW | 05.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Afghanistan 40 sun ji rauni sakamakon tashin wani bam kusa da motarsu.

3. Sojojin Afghanistan 40 sun ji rauni sakamakon tashin wani bam kusa da motarsu.

Rahotannin da suka iso mana baga birnin Kabul na Afghanistan, sun ce sojojin ƙasar 40 ne suka ji rauni, yayin da aka ta da bam kusa da bas ɗin da ya kwashe su zuwa aiki yau da safen nan. Ma’aikatar tsaron ƙasar ta ce wasu ma’aikatan gwamnati guda 7 kuma sun ji rauni, su ma yayin da bam ya tashi kusa da motar da suke ciki a kan hanyarsu zuwa aiki.

A kwanakin bayan nan dai, ’yann ƙungiyar Taliban sun tsananta hare-haren da suke kai kan kafofi da jami’an gwamnati da kuma sojojin mamaye na ketare da ke girke a ƙasar, musamman a jihohin kudanci da gabashin Afghanistan ɗin.