1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun yi mubai´a ga saban shugaban ƙasar Turkiyya Abdullahi Gül

August 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuCo

Saban shugaban ƙasar Turkiyya Abdellah Gül, ya yi ganawar farko da rundunar sojoji ta ƙasa.

Gül da shugaba rundunar Janar Yasar Büyükanit sun yi musabaha,

da farko sojoji sun nuna adawa da zaɓen Abdellah Gül a matsayin shugaban ƙasa, tare da bada hujar cewar, ya na da tsatsauran ra´ayin adinin islama, abunda kundin tsarin mulkin ƙasar Turkiyya bai amince da shj ba.

Abdellah Gül, ya yi alkawarin raba harakokin siyasa da na addini a zamanin mulkin sa.

A halin yanzu dai ya na ci gaba da samun saƙƙwanin taya murna, daga sassa daban-daban na dunia.

A yau Amurika, Russia, da ƙungiyar haɗin kann larabawa, sun yi lale marhabin da shi a wannan muƙami.

Idan dai za a iya tunawa, jiya ne majalisar dokoki ta zaɓi tsofan ministan harakokin wajen Turkiyya, Abdellah Gül a matsayin shugaban ƙasa bayan wata da watani ana kai ruwa rana.