1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun bindige 'yar ƙunar bakin wake a Maiduguri

Salissou BoukariOctober 18, 2015

A ƙoƙarin da suke na daƙile yunƙurin 'yan ta'adda masu kai hare-hare a Tarayyar Najeriya, sojojin ƙasar da ke barakin soja na Maimalari a birnin Maiduguri, sun yi nasarar kawar da wani hari.

https://p.dw.com/p/1GqA8
Hoto: -/AFP/Getty Images

Da misalin ƙarfe bakwai ne dai na safiyar wannan Lahadin agogon Najeriya, wata mata ɗauke da wani ƙunshi taq yi yunƙurin shiga barakin sojan na Maimalari da ke Maiduguri kuma duk da kira da sojan da ke tsaro ya yi zuwa gareta na ta dakata amma kuma ta yi ƙememe, abin da ya kai ga buda mata wuta inda nan take jakar da ke tare da ita ta tarwatse tare da hallakata ita kadai.

Mayaƙan Ƙungiyar Boko Haram dai sun rubunya kai hare-harensu a 'yan watannin baya-bayan nan, inda a wannan makon ka dai suka yi sanadiyyar hallaka mutane 37 a birnin na Maiduguri.