1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji kananan yara a nahiyar Afirka.

Mohammad Nasiru AwalNovember 20, 2003
https://p.dw.com/p/BvnY
Kimanin shekaru 14 da suka wuce lokacin da aka fara samun labari daga kasar Liberia cewa kananan yara a wannan kasa na aikata kisan kai, duniya gaba daya ta kadu, kuma har yau ba´a manta da hakan ba. Hasali ma yawan sojoji kananan yara ya karu ne zuwa sama dubu 300. China Keitesi daga kasar Uganda, tun tana ´yar shekara 9 da haihuwa take yiwa ´yan tawayen wannan kasa bauta. Ta shafe shekaru 10 a hannun ´yan tawayen kafin Allah Yayi mata gyadar dogo ta shigo nahiyar Turai. Ita dai China kamar sauran dubban matasa a yankunan karkara na kasar Uganda, ta tsere daga hannun ´yan tawayen kungiyar Lord Resistance Army zuwa alkarya. Ita dai wannan kungiya ta yi kaurin suna wajen sata kananan yara kuma tana tilasta su daukar makami.
China Keitetsi ta ce babbar matsalar dai ita ce ga kananan yaran shiga aikin sojin wata hanya ce ta samun abin sakawa bakin salati, kuma daukaci zaka tarar ba su da wurin zuwa. Kuma kasancewar su a cikin sojojin ´yan tawaye ko sun koma gida babu mai son yayi wata hulda da su.
Abin da ke jawo hakan dai shine bayan an tilasta su shiga aikin soji, ana ba su abubuwa masu sa maye, sannan a lokuta da dama akan tilasta musu kashe danginsu ko ma iyayensu. Bayan haka ne kuma sai kisan kai ya zama musu jiki.
A dai halin da ake ciki kungiyoyi da hukumomi sun fara daukar matakai da nufin bayanawa duniya irin mawuyacin hali da yaran kan tsinci kansu a ciki. Alal misali wasu kungiyoyin Jamus tare da hadin guiwar takwarorinsu na yankin Gabashin Afrika na tafiyar da wani aiki bisa manufar ceto wadannan yara daga halin kaka-ni-kayin da su kan shiga. Yanzu haka dai masu ba da taimakon agaji na kasa da kasa na taimakawa don sake shigar da wadannan yaran cikin jama´a. To sai dai matsalar da ake fuskanta a nan ita ce, daukacin yaran na shiga kungiyar ´yan tawayen ne don radin kansu ko kuma saboda dalilai na talauci.
A halin da ake ciki akwai kananan bindigogi samfurin kalashnikov kimanin miliyan 600 a duk fadin duniya. Da irin wadannan makaman ne kuwa ake horas da sojoji kananan yara. Kasashen da ke kera makaman ciki har da nan Jamus, na tura makaman zuwa kasashen da ba na kungiyar EU ba. A dangane da haka kungiyoyin ba da agaji ke yin kira da dauki kwararan matakai don hana irin wadannan makaman fadawa hannun kungiyoyin ´yan tawaye da gwamnatoci dake daukar kananan yara aikin soji. A rikicin Kongo alal misali akwai sojoji kananan yara kimanin dubu 30 a bangarorin ´yan tawaye da kuma gwamnati. Wani abin takaici kuma shine da kudin taimakon raya kasa da ake ba wadannan kasashen ne ake juya akalar su wajen sayen makamai.
Ko da yake a halin nan da ake ciki da wuya a iya ceto kananan yara daga rikice-rikicen da ake fama da su, amma ranar yara ta duniya da aka ware a duk shekara, babbar dama ce a yunkurin da ake yi na kwance damarun kananan yara.