Sojoji a Senegal na zaben shugaban kasa | Labarai | DW | 17.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji a Senegal na zaben shugaban kasa

Ayau ne sojojin kasar Senegal suke kada kuriunsu a karon farko da samun yancin kasar shekaru 47 da suka gabata ,inda suke zaban shugaban kasa ,mako guda gabannin sauran alummomin wannan kasa.Shugaba Maici kuma,mutumin da ake ganin shine zai lashe zaben Abdoulaye Wade,ya yiwa dokokin zaben wannan kasa dake yankin yammacin Afrika garon Bawul,domin bawa sojojin damar kada kuriunsu,yau asabar zuwa gobe lahadi.A ranar 25 ga wannan wata nedai sauran alummomin Senegal din zasu kada nasu kuriun.Senegal dai itace kasa daya, ayankin yammacin Afrika da bata taba fuskantar juyin mulki ba tun bayan samun yancin kai daga Faransa,kuma dakarun kasar na gudanar da harkokin rayuwarsu a tsakanin sauran alummomi.Mafi yawan jamaar kasar dai sun yi mamakain wannan mataki da shugaba Wade ya dauka,mutumin da ke fuskantar sukan karuwan rashin aikinyi da rashin ingantuwan kayayyakin rayuwa.