Sojoji 5 na FINUL sun mutu a Libanon. | Labarai | DW | 24.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji 5 na FINUL sun mutu a Libanon.

Sojoji 5 na rundunar ƙasa da ƙasa ta Finul ,su ka rasa rayuka, wasu kuma karin 3 su ka ji mummunan raunuka a sakamakon fashewar wata bam a kudancin Libanon.

Rahotanin sun nunar da cewa, dukkan sojojin yan asulin ƙasar Spain ne.

kakakin rundunar ta Majalisar Ɗinkin Dunia, da ke gudanar da ayyukan tsaro a Libanon, ya tabbatar da wannan alƙalluma,sannan Milöos Strugar ya ce, sun tura tawagar ƙurraru domin ƙarin haske a game da faruwar al´ammrin.

Majalisar Ɗinkin Dunia,ta tura runduna a ƙasar Libanon, domin kulla da yarjejniyar da a ka cimma, tsakanin Isra´ila da mayaƙan Hizbullahi na ƙasar Libanon, bayan yaƙin da su ka gwabza a shekara ta 2006.

A wani labarin kuma, da ya shafi Libanon ana ci gaba da ɓarin wuta, tsakanin sojojin Gwamnati da dakarun ƙungiyar Fatah Al Islam.