Sojoji 4 sun rasa rayuka a Afghanistan. | Labarai | DW | 23.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji 4 sun rasa rayuka a Afghanistan.

A yankin Khandar na Afganistan, sojoji 4 na ƙasar Kanada sun rassa rayuka a cikin hare-haren yan taliban.

A yayin da ya ke taron manema labarai, a game da wannan ƙarin mace- mace, shugaban rundunar Canada Jannar Rick Hillier,ya bayyana cewar, wata Bam ce, mai ƙarfin gaske, ta fashe, gap ga wucewar ayarin sojojin su.

Daga shekara ta 2002 zuwa yanzu, Canada ta yi assara sojoji 15 a ƙasar Afganistan.

Saidai duk da assarorin rayuka, da su ke samu, Jannar Hillier, ya bayana cewa, sojojin Canada, za su ci gaba, da zama a ƙasar Afganistan, domin taimakawa talakawa, da ke fuskantar hare –hare, daga yan taliban.