Sojin Najeriya 8 sun mutu a arangama da BH | Labarai | DW | 10.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Najeriya 8 sun mutu a arangama da BH

Rundunar sojin Najeriya ta ce ba za ta saurara ba yakin da ke yi da yan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar har sai ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin baki daya.

A kalla sojojin Nijeriya 8 ne suka rasa ransu a wani musayar wuta tsakanin su da 'yan kungiyar Boko Haram a Borno a wannan juma'ar.

'Yan Boko Haram din sun kai wani samame garin Ajirin da ke Mafa kilmita 50 daga babban birnin jihar,inda suka bude wuta tare da tashin bama bamai wanda yayi sanadiyayr rasuwar jama'a tare da jikkatar wasu.

A 'yan kwanakin nan dai kungiyar ta Boko Haram na ci gaba da kai hare hare a garuruwa daban daban a yankin arewa maso gabashin Najeriya duk kuwa da fatattakar su da rundunar sojin kasar ta yi daga sansanin dajin Sambisa