1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin mamaye za su bar Iraƙi

Faraministan IraƙI Nuri- Al Maliki ya ce a shekara ta 2008 ne aikin sojin kiyaye zaman lafiya ƙarƙashin laimar Majalisar Ɗinkin Duniya ke ƙarewa a ƙasar.Bayan ficewarsu a cewar Mr Maliki, Iraƙi da mahukuntan Amirka za su ƙulla wata sabuwar yarjejeniya ta aikin kiyaye zaman lafiya a ƙasar. Rahotanni sun nunar da cewa tuni shugabannin biyu, wato Mr Bush da Al-Maliki sukayi nisa wajen tattauna wannan batu. Za a ci gaba da wannan tattaunawa ne a cewar mahukuntan na Amirka a farko-farkon sabuwar shekara, a kuma kammala a watan yuli. Dakarun sojin kiyaye zaman lafiyar na tafiyar da aikin su ne a Iraƙin ƙarƙashin jagorancin ƙasar ta Amirka ne.