1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Israila sun kashe wani shugaban Islamic jihad

Dakarun Israila sunce su kashe wani shugaban kungiyar Islamic Jihad a Jenin dake yamma da gabar kogin Jordan.Majiyoin tsaro daga yankin Palasdinawa sunce sojojin na Israila sunyi shiga irin ta Palasdinawa a lokacinda suka jenin inda suka kashe Abu Srour tare da raunata wani dan kungiyar.Wata mai magana da yawun sojin Israilan ta tabbatar da cewa dakarunsu sun kai hari kann wata mota dake dauke da wasu yan bindiga uku.Israilan dai tace irin wadannan hare hare suna taimaka mata kare kai hari kann jamaarta,yayinda shugabanin Palasdinawa suka ce hare haren suna lahani ga batun zaman lafiya a yankin.Koda a jiya jumaa sojojin Israila sun kashe wani dan shekaru 13 a kauyen Seida a yamma da gabar kogin Jordan.