Sojin Israila ba zasu shiga garuruwan Palasdinawa ba a lokacin zabe | Labarai | DW | 23.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Israila ba zasu shiga garuruwan Palasdinawa ba a lokacin zabe

Kafofin yada labarai na Israila sun bada rahotannin cewa,sojojin kasar ba zasu kasance a garuruwan Palasdinawa ba a yankin yamma da gabar kogin Jordan cikin kwanaki 3 masu zuwa,domin kare shiga sharo ba shanu a zaben majalisar dokokin Palasdinu na ranar 25 ga wannan wata da muke ciki.

Gidan rediyoyn Israilan yace,sojojin zasu dakatar da kai farmaki sai dai sun tabbatar da akwai wani hadarin kai masu hari,ko kuma samun rahoton kaiwa harin.

Hakazalika sojojin ba zasu shiga garuruwan Palasdinawa ba karkashin wani shiri da suka lakabawa suna Operation White Winter.