Sojin Iraƙi sun halaka masu ta da ƙayar baya 30 a Bagadaza | Labarai | DW | 07.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Iraƙi sun halaka masu ta da ƙayar baya 30 a Bagadaza

Gidan telebijin gwamnatin Iraqi ya rawaito sojojin kasar na cewa sun kashe ´yan tawaye kimanin 30 a wata musayar wuta da aka yi a tsakiyar birnin Bagadaza. Sojojin sun ce sun kuma kame mayakan ´yan tawaye 6. Gumurzun na matsayin somin tabin na sabbin tsauraran matakan da gwamnati ke dauka kan ´yan takife. FM Nuri al-Maliki ya sha alwashin sa kafar wando guda da sojojin sa kai na ´yan sunni da shi´a wadanda ke da hannu a da yawa daga cikin munanan tashe tashen da suka ki ci suka ki cinyewa. A cikin sa´o´i 24 gabanin jiya da yamma ´yan sanda sun gano gawawaki 71 a unguwannin da ke birnin Bagadaza. A wani labarin kuma an kashe sojojin Amirka biyu, daya a Bagadaza daya kuma a yammacin kasar Iraqi.