1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin gwamnati na ci-gaba da kai farmaki kan ´yan tawaye a Sri Lanka

´Yan tawayen Tamil Tigers na kasar Sri Lanka sun ce zasu mayar da martani akan gwamnati idan aka ci-gaba da kai farmaki da jiragen saman yaki da bindigogin atileri akan yankin su. Wani babban jami´in ´yan tawayen kungiyar ´yanto Tamil Eelam, S. Puleedevan ya fadawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa farar hula da dama sun mutu sannan wasun su na tserewa daga hare-haren jiragen saman gwamnati wanda aka fara bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai a birnin Colombo a jiya talata. Ana zargin ´yan tawayen da hannu a wannan hari, wanda wata mace da ta badda kama kamar mai juna biyu ta kai. Akalla mutane 10 suka rasu sannan 26 suka samu raunuka ciki har da wani kwamandan sojin Sri Lanka, wanda ya ji mummunan rauni. A halin da ake ciki sojin kasar na kai farmaki kwana biyu a jere akan wuraren ´yan tawaye dake arewa maso gabashin kasar.