1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SOJIN BRITANIA SUN BAR BASRA ZUWA AREWACIN BAGADAZA.

October 27, 2004
https://p.dw.com/p/Bvf8
Ayarin Dakarun Britania daga Basra zuwa arewacin kasar.
Ayarin Dakarun Britania daga Basra zuwa arewacin kasar.Hoto: AP

A yau ne ayarin Dakarun Britania dake birnin Basran Iraki suka doshi arewacin kasar ,domin mamaye wani yankin rikici dake kusa da birnin Bagadaza,tare da maye gurbin sojin Amurka dake diban kashinsu a hannu dangane da harin yan ta kifen Falluja.

Bayan da gwamnatin Tony Blair na Britania ta amince da bukatun Amurka na sauyawa Dakarunta matsuguni daga sansaninsu dake Basra,zuwa yankunan da ake cigaba da bata kashi tsakanin Dakarun Amurka da Sojojin sari ka noken Iraki,rahotanni dake iso mana na nuni dacewa a yanzu haka ayarin dakarun na britani sun doshi arewacin kasar Iraki,ata bakin Squadron Leader Steve Dharamraj daga Basra.

Dankarun dai sun samu kariya dangane da koda wane irin harin Gurneti yan sari ka noken ka iya afka musu da ita.Kimanin Dakarun Britaniayan 850 ake saran zasu kasance a kudancin Bagadaza,akasarinsu kuwa daga rundunar Black Watch Regiment,domin bawa dakarun Amurkan daman fuskantar rikicin garin Falluja dayaki ci yaki cinyewa.amurkawan dai sun dauki alkawarin shawo kann rikicin garin na yan Sunni ta kowace hanyan,bayan da gwanatin rikon kwaryan Irakin a hannu guda ta lashi takobin tabbatar da zaman lafiyan fallujan kafin zaben kasar dazai gudana a watan janairun shekara mai zuwa.

Majiyar Sojin dai na nuni dacewa wani Bomb da aka dana a jikin Babur ya ritsa da ayarin dakarun Amurkan,inda guda daga cikinsu ya sheka lahira ,banda guda daya jikkata ,a arewacin Bagadaza.

Jamian Amurkan dai sun sanar dacewa ana laakari da kara tura wasu karin sojoji zuwa Irakin saboda shirye shiryen zabe,ta hanyar jinkirta tafiyan wasu domin bawa sabbin daman maye gurabansu.

Yanzu haka dai Daruruwan iyalai sun fice daga garin na Fallujan ,domin kare rayukansu,ayayinda ayau ne magabatan garin ke shirin komawa bagadaza domin,domin ganawa da gwamanti kann yandda zaa warware wannan rikici.Gwamnati a hannu guda tayi alkawarin ganin karshen wannan rikici koda kuwa amfani da karfin Soji ne,sai dai idan har magabatan garin sunsun mika Abu Musab al-Zarqawi,wanda ake zargi da kasancewa a fallujan.

A jiya ne kungiyar Al Zarqawin tayi barazanar fille kann wani dan Japan datayi garkuwa dashi,idan har Japan din bata janye dakarun ta 550 dake Irakin ba cikin saoi 48.Dayake mayar da martani yau,prime minista Junichiro Koizumi na Japan yace ko kadan kasar sa bazata janye dakarunta daga iraki ba,duk da wannan barazanar.Wannan yanayi dai ya jefa shugaban gwamnatin Japan cikin rikicin siyasa,wanda tun a bayan alummar kasarsa sukayi adawa da tura dakarun zuwa Irakin.

A hannu guda kuma wani babban jamiin kimiya na Irakin Mohammad al-Sharaa,ya karyata zargin da akeyi nacewa makaman nan da suka bace ,sun bace ne tun kafin kifar da gwamantin Sadam a bara.A wannan makon nedai hukumar lura da makamashi ta mdd ta sanar da bacewan wadannan makamai,bayan an kifar da gwamnatin Sadam a watan Afrilun shekarar data gabata.Ayayinda bacewan makaman ya mamaye siyasar Amurka,gabannin zabe,wasu jamian Amurkan sunyi hasashen cewa ,tana iya yiwuwa an sace wadannan makamai ne kafin dakarun Amurkan su fada Bagadaza da yaki.

Zainab Mohammed.