Sojin AU ɗaya ya rasa rai a Somalia | Labarai | DW | 01.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin AU ɗaya ya rasa rai a Somalia

A ci gabada gumurzu tsakanin rundunbar gwamnati Somalia da yan yakinsari ka noke, a karro na farko, rundunar shiga tsakani ta Tarayya Afrika ta yi assara soja daya dannkasar Uganda.

Tun ranar alhamis da ta wuce, ɓarin wuta ya turnuƙe a birnin Mogadiscio, a dalili da matakin da haɗin gwiwar dakarun gwamnatin Somalia, da na Ethiopia su ka ɗauka na tsabttace birnin daga hare-haren dakarun kotunan Islama.

Rahottani daga ƙasar sun ce, halin yanzu asibitocin ƙasar baki ɗaya ,sun cika sun bace da mutanen da su ka samu raunuka, a sakamakon wannan arangama, Sannan dubun-dubunan jama´a, sun shiga halin gudun hijira domin tsira da rayuka.

Idan dai ba manta ba, cemma kakakin rundunar kotunan Islama, wanda da aka kora daga birnin Mogadiscio, a watan januari da ya gabata, sun yi kashedi, ga sojojin taraya Afrika na kadda su shiga Somalia, domin za ta zama ajalinsu, inji shugabanin kotunan Islama.