Sojin Amurka dana Iraqi sun kara da yan bindiga a Diwaniyah
October 8, 2006Talla
Rundunar sojin Amurka dana Iraqi sun kara da gungun yan bindiga a garin Diwaniyah dake kudancin Iraqi.
Babu dai cikakken rahoto game da wadanda suka jikkata sai dai wadanda suka ganewa idonsu sunce tankuan yaki suna sintiri a cikin birnin yayinda jirage masu saukar angulu je shawagi a sasarin saman birnin na Diwaniyah.
Tashe tashen hankulan sun fara ne da asubahin yau,yayinda sojojin Amurka dana Iraqi suka ci karo da nakiyoyi da aka binne lokacinda suka kai hari a garin.
Yanzu haka dai an kafa dokar hana fita a garin na Diwaniyah,inda a watan agusta aka fafata tsakanin magoya bayan moqtada as sadr da sojin Iraqi,inda mutane da dama suka rasa rayukansu.