1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Amirka sun gaza a Iraƙi…

Mataimakin shugaban ƙungiyyar Al-Qaida, Ayman Al-Zawahri ya ce sojin Amirka a Iraƙi sun gaza. Hakan a cewar Al-Zawahri ya sa sojin Amirka na neman tserewa daga Iraƙin. Al-Zawahri, wanda ya aike da wannan sako ga yanar gizo-gizo ta Internet, ya tabbatar da cewa Al-Qaida na ci gaba da karɓuwa a Iraƙi. Shugaban na Al-Qaida ya kuma ce har yanzu sojin Iraƙi ba su da ƙarfin ikon tabbatar da tsaro da oda a ƙasar, kamar yadda sojin mamaye ke cewa. Sakon na Al-Zawahri ya zo ne a dai dai lokacin da Biritaniya ta kammala miƙa Garin Basra ga sojin na Iraƙi.