1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soji sun yi wa gidan Mugabe kofar rago

Zainab Mohammed Abubakar | Abdul-raheem Hassan
November 15, 2017

Kafar talabijin ta kasar Zimbabuwe ya fara yada shirye-shirye, bayan da sojoji suka karbe iko da shi a wani yunkuri na dai-daita lamuran siyasa.

https://p.dw.com/p/2ngOn
Robert Mugabe
Hoto: AFP/Getty Images

Mai magana da yawun rundunar sojin Zimbabuwe ya tabbatar da cewa shugaba Mugabe da iyalinsa na cikin koshin lafiya, sun kuma karyata yunkurin kifar da mulki. Shugaban gamayyar kasashen yankin kudancin Afrika, kuma shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya yi kira ga rundunar tsaro da gwamnatin kasar Zimbabuwe da su gaggauta warware matsalar da ta kunno kai cikin kasar.

Ehemaliger Finanzminister Simbabwes Tendai Biti
Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Tendai Biti Hoto: AFP/Getty Images/J. Nijikizana

Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP kuma tsohon ministan kudi na Zimbabuwe Tendai Biti ya ce duk da cewar suna Allah wadan amfani da karfi wajen karbar madafun iko, ya zama wajibi a yi la'akari da abubuwa biyu, ya ce: " Da farko babu wani tashin hankali, domin ina ganin sojojin sun dauki lokaci wajen shirya hakan a tsanake. Mun tabbatar da cewar babu asaran rai kuma babu wani dan Zimbabuwe da rayuwarsa ke cikin hatsari. Na biyu muna sane da cewar akwai matsalolin da buktar a magancesu a kasar. Sun hada da na tattalin arziki da siyasa ,wadanda ke da alaka da shugaba Mugabe, daura da wanda zai gaji kujerarsa".

Emmerson Mnangagwa und Robert Mugabe in Simbabwe
Emmerson Mnangag, tsohon mataimakin shugaba Mugabe da mai dakinsaHoto: Getty Images/AFP/J. Njikizana

Robert Mugabe mai shekaru 93 a duniya ya jima ya na cin karensa babu babbak a jam'iyyarsa ta ZANU-PF mai mulki, kuma bisa dukkan alamu ko ba duka ba da yawa daga cikin 'yan jam'iyyar na mara masa baya saboda dalilai na siyasa. Batu da baya-bayannan ya tayar da hankali a cikin kasar shi ne korar mataimakinsa da aka yi gwagwarma da shi, Emmerson Mnangagwa  a ranar 6 ga watan Nuwamba tare da tsara maye gurbinsa da mai dakinsa Grace, wanda sharar fage ne a matsayin wadda zata gaji kujera tasa.

Simbabwe Krise Straßenszenen aus Harare
Sojoji na iko da tsakiyar birnin HarareHoto: Reuters/P. Bulawayo

Kungiyar ta SADC na shirin tura jakadunta guda biyu da suka hada da mininistan tsaro da karamin minista a ma'aikatar tsaron Afirka ta Kudu zuwa birnin Harare. Mai bincike a cibiyar ISS da ke Pretoria Lies Louw-Vaudran ta ce haluin da ake ciki a zibabuwe ya dade ya na ciwa Kungiyar SADC tuwo a kwarya, a matsayinta na mai shiga tsakani, ta ce: "Da yawa daga cikin 'yan Zimbabwe sun bar kasarsu zuwa Afirka ta Kudu saboda matsalolin tattalin arziki, yanzu idan akwai rikicin siyasa, yawansu zai karu. Matsalar za ta shafi har Botswana da Mozambique, musamman barkewar tashin hankali a Zimbabwe".

A daidai lokacin rundunar sojin ke jaddada cewar su na kokarin daidaita lamura ne amma ba juyin mulki ba, wasu na jaddada bukatar sauke shugaba Robert Mugabe ba wai daga kujerar mulki kadai ba, har ma daga shugabancin jam'iyyar ZANU-PF mai mulki.