Sojan kiyaye zaman lafiya na MDD | Siyasa | DW | 04.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sojan kiyaye zaman lafiya na MDD

A yayinda a bangare guda sojan kiyaye zaman lafiya ke shan yabo a daya bangaren kuma suna shan tofin Allah tsine game da ayyukansu

Hular sojan MDD

Hular sojan MDD

Babban misali a nan dai shi ne kasar Liberiya, inda ake yaba wa sojan kiyaye zaman lafiyar na MDD dangane da rawar da suka taka wajen hana dan kama-karya Charles Taylor komawa kann karagar mulki da kuma taimakawa wajen zaben mace da farko dake shugabantar kasar bayan kawo karshen yakin basasar da tayi shekara da shekaru tana fama da shi. Ko da yake akwai masu duban ayyukan sojojin kiyaye zaman lafiyar ta fuskoki guda biyu, amma jami’an MDD sun sikankance cewar shekarar da ta gabata ta 2005 da kasancewa shekara mai nasara, musamman ma idan aka yi la’akari da kammala ayyukan kiyaye zaman lafiyar a yankin East Timor da kuma kasar Saliyo. Bayan taimakawar da suka yi wajen sake tsugunar da mutane sama da dubu 200 a garuruwansu na asali dake East Timor, a ranar asabar da ta wuce sojojin kiyaye zaman lafiyar na MDD suka kawo karshen aikinsu na tsawon shekaru shida a wannan yanki. Kazalika bayan aikin kiyaye zaman lafiya na tsawon shekaru shida domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Saliyo a yanzun an janye sojojin majalisar daga kasar ta yammacin Afurka dake shirin gudanar da zabe a shekara mai zuwa ta 2007. Dangane da wannan ci gaba da aka samu, jami’an majalisar dinkin duniyar ke tattare da ra’ayin cewar wajibi ne a yaba mata a game da rawar da take takawa yanzu haka a kasar Afghanistan domin share hanyar zaben kasar da za a gudanar a wannan shekara. Suka ce wannan wata babbar nasara ce a wannan kasa, wadda tayi shekara da shekaru tana fama da tashe-tashen hankula. Dangane da zargin da ake wa sojan kiyaye zaman lafiyar a game da yi wa mata fyade a kasar Kongo da kuma kisan gilla akan farar hula a kasar Haiti kuwa, jami’an cewa suka yi, tuni aka kammala binciken wasu mutane 200 a game da laifin yi wa mata fyade kuma a halin yanzu haka ana ba da horo na musamman ga dakarun sojojin domin kyautata halayensu. Bugu da kari kuma tuni aka gurfanar da ainifin sojojin dake da laifukan fyaden gaban shari’a.

A dai halin da muke ciki yanzu MDD na da jami’an kiyaye zaman lafiyarta sama da dubu 80 da suka hada da sojoji da ‚yan sanda da kuma farar hula a kasashe daban-daban har 17. Kimanin kashi 80 cikin dari na sojojin sun fito ne daga kasashe matalauta, saboda kasashen dake da wadatar arziki na dari-dari wajen ba da gudummawar sojojinsu, musamman ma tun bayan rashin nasarar aikin kiyaye zaman lafiyar a kasar Somaliya a shekara ta 1990.