1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojan kiyaye zaman lafiya a Kongo

April 27, 2006

Kungiyar Tarayyar Turai ta tsayar da shawarar tura sojan kiyaye zaman lafiya zuwa Kongo

https://p.dw.com/p/Bu0R
Sojan MDD a Kongo
Sojan MDD a KongoHoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Da yawa daga cikin wakilan majalisar dokokin Jamus ta Bundestag na saka ayar tambaya a game da amfanin wannan mataki dake da nufin tura sojojin kiyaye zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Turai su 1500, abin da ya hada har da sojojin Jamus 500 da zasu sa ido akan zaben kasar Kongo. Duka-duka aikin kiyaye zaman lafiyar ba zai zarce watanni hudu ana gudanar da shi ba, in ji ministan tsaron Jamus Franz-Josef Jung. Ya ce kuma ko da yake yawan sojojin bai taka kara ya karya ba, amma aikin zai zama mai cikakken tasiri. Jung ya ci gaba da cewar:

Ina fatan cewar wannan matakin, wanda ke da nufin sa ido akan zaben kasar Kongo zai zama mai tasiri ya kuma taimaka wajen bai wa kasar wani takamaiman tsari na mulkin demokradiyya tsantsa.

Ko da yake za a tsugunar da sojojin na Jamus a fadar mulki ta Kinshasa ne kawai, amma ana fata matakin zai zama na gama gari ne domin ya hada da sauran sassa na kasar ta Kongo. Jung dai ya ce sojojin Faransa ne za a dora musu alhakin kula da duk wani matakin da zai kai ga kwashe jama’a a wajen birnin na Kinshasa. To sai dai kuma shugaban kungiyar sojan Jamus Bernhard Gertz ya bayyana tababarsa a game da fa’idar wannan mataki duk da wannan gata da za a yi wa sojojin Jamus na kebesu daga duk wata arangama da ka taso a wajen birnin Kinshasa inda yake cewar:

Kasar ta nika Jamus har sau shida kuma dukkan hanyoyinta na sadarwa sun tabarbare. Ta la’akari da haka wannan mataki na nuna alfarma ne ga fadar mulki ta Kinshasa, amma ba zai yi wani tasiri na a zo a gani ba.

Masu sukan lamirin matakin dai suna nuni da kasada da kuma bashin dake tattare da shi alhali ba wani mataki ne mai tasiri ba. Amma duk da haka ministan tsaro Franz-Josef Jung na sa ran samun cikakken goyan baya daga majalisar dokoki ta Bundestag, inda yake cewar:

Ina kyautata imanin cewar akasarin wakilan majalisar zasu yi na’am da wannan mataki, saboda ita kanta Jamus ma zata ci gajiyarsa. Da farko dai saboda makobtakar Afurka da Turai. Ba shakka zamu ci gaba da fama da matsalar ‘yan gudun hijira saboda makurdadar Gibralter bata da fadi.

A daya bangaren dai masu goyan bayan matakin na tattare da ra’ayin cewar kasar Kongo zata samu zaman lafiyxa da kwanciyar hankali ne idan masu asarar zaben da za a gudanar ba su yi amfani da karfin bindiga domin nuna adawarsu da sakamakonsa ba. Wannan kuma shi ne ainifin makasudin tura sojojin kiyaye zaman lafiyar na Kungiyar Tarayyar Turai domin kandagarkin billar irin wannan tashe-tashen hankula bayan zaben.