Sojan ISAF ɗaya ya rasa rai a Afghanistan | Labarai | DW | 03.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojan ISAF ɗaya ya rasa rai a Afghanistan

Dakarun Taliban na kudanci Afghanistan ,sun kashe ƙarin soja ɗaya na rundunar ƙasa da ƙasa ta ISAF, a sahiyar yau almahis.

Sojan ya rasa ran sa sanadiyar, tarwasewar wata Bom, a kussa da Khandar.

Wannan shine soja na 4 da ya mutu a ƙasar, tun bayan da ƙungiyar tsaro ta NATO, ta ɗauki jagorancin ayyukan sojojin ƙasa da ƙasa a Afgahanistan, ranar litinin da ta wuce.

An ɓangaren yan taliban, rundunar ISAF ta bayyana kashe mayaƙa a kalla 10 tsakanin jiya zuwa yau.