1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojan ISAF ɗaya ya rasa rai a Afghanistan

August 3, 2006
https://p.dw.com/p/Buo3

Dakarun Taliban na kudanci Afghanistan ,sun kashe ƙarin soja ɗaya na rundunar ƙasa da ƙasa ta ISAF, a sahiyar yau almahis.

Sojan ya rasa ran sa sanadiyar, tarwasewar wata Bom, a kussa da Khandar.

Wannan shine soja na 4 da ya mutu a ƙasar, tun bayan da ƙungiyar tsaro ta NATO, ta ɗauki jagorancin ayyukan sojojin ƙasa da ƙasa a Afgahanistan, ranar litinin da ta wuce.

An ɓangaren yan taliban, rundunar ISAF ta bayyana kashe mayaƙa a kalla 10 tsakanin jiya zuwa yau.