Sojan da ke yakar IS sun bude wuta a Raqa | Labarai | DW | 04.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojan da ke yakar IS sun bude wuta a Raqa

Babban burin fadan dai na zama na ganin an kwace kafatanin yankin da IS ke iya tasiri a birnin Raqa da ke Siriya da tuni ake fafatawa da mayakan na IS tun a shekarar bara.

Dakarun Kurdawa da Larabawa da ke samun goyon bayan Amirka a Arewacin Siriya sun bayyana a ranar Asabar din nan cewa sun kaddamar da sabbin hare-hare kan mayakan IS a wasu garuruwa da kauyuka da ke Arewacin birnin Raqa. Sojan gwagwarmayar kare dimukaradiyya sun bayyana a ranar Asabar din nan cewa sun koma filin daga, a ta bakin Cihan Sheikh Ehmed da ke magana da yawun dakarun , ta ce sun shiga kaso na uku na fafutikar kwace Raqa fadan da aka fara tun a watan Nuwambar bara.

Babban burin fadan dai na zama na ganin an kwace kafatanin yankin da IS ke iya tasiri a birnin. Wannan jawabi dai na zuwa ne kwana guda bayan da jirgin sama bisa jagorancin Amirka ya yi raga-raga da wata gada a wannan yanki da kungiyar ta IS ke taka rawar gaban hantsi.