Sojan Amirka ya mutu a haɗarin mota a Iraqi. | Labarai | DW | 01.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojan Amirka ya mutu a haɗarin mota a Iraqi.

Wani rahoton da muka samu ɗazu-ɗazun nan ya ce, hukumar sojin Amirka a Iraqin ta tabbatad da mutuwar ɗaya daga cikin sojojinta, wwaɗanda suka yi haɗari cikin motarsu a garin Mosul da ke arewacin ƙasar. Hukumar ta ce tun ran asabar ne aka yi haɗarin, amma ba ta ba da ƙarin haske game da yadda ya auuku ba. Kawo yanzu dai yawan sojojin Amirka da suka rasa rayukansu a Iraqi, ya kai dubu 2 da ɗari 7 da 7, bisa alƙaluman ma’aikatar tsaron Amirkan, wato Pentagon.